Shugaba
Vladimir Putin na kasar Rasha ya bukaci gwamnatin kasar da ta
bada agaji ga Sabiyawa marasa rinjaye a yankin Kosovo.
A zaman
majalisar ministocin kasar a ranar Litinin din nan, ministan
harkokin wajen kasar Sergei Lavrov ya bayyana cewa gwamnatin
kasar na bukatar abinci,magunguna,dama wasu kayayyakkin aiki na
lafiya.