Shugaban
Sabiya Mr Boris Tadic ya rusa majalisar dokokin kasar tare da
ware ranar 11 ga watan mayu domin gudanar da zabe.
Matakin ya
biyo bayan durkushewar da gwamnatin Hadaka karkashin jagornci na
Firayminsta Vojislav Kostunica ta yi a makon da ya gabata.
Ministocin
Sabiya sun kasa cimma daidaito kan jingine huldar zumunci da
Kungiyar tarayyar kasashen Turai wato .E.U. domin nuna korofi ga
amincewa da yancin Kosovo da wasu mambobin kungiyar ta E.U. suka
yi.
Rundunar
sojojin Pakistan ta yi tirr da dakarun kawance karkashin
jagoranci na kasar Amurka sabili da harba makami mai kunsau na
atilare a iyakar Pakisatan da ya kashe mata biyu da wasu kananan
yara guda biyu.
Mai Magana
da yawun rundunar sojojin Manjo-Janar Athar Abbas ya ce dakarun
kawance wadanda ke fafatawa da yan gwagwarmaya, sun jefa makami
mai kunsau daban-daban guda biyar da suka afkawa lardin
Waziristan dake yankin arewaci.
Dakarun
Amurka sun ce harin wani martini ne ga wata barazanar da aka
hakikance.
Sojojin Amurka da na Pakistan suna gwabza fada da mayakan
sunkuru na Taliban a iyaka dake tsakanin kasashen Afghanistan da
Pakistan.