Hausa Archive

 
Search Engine
 
 

Shafi.......................... Nijeriya ............... Afrika............... labaran duniya

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

 

Shugabannin jamiyyun siyasa guda biyu da suka yi nasara a zabubbukan kasar Fakistan sun rattaba hannu akan yarjeniyoyin kafa gwamnatin hadaka a kasar.

Mijin tsohuwar firaminista marigayyiya Benazir Bhutto wato,Asif Ali Zardari da kuma tsohon Firayminista Nawaz Sherif sun bukaci shugaba Pervez Musharraf da ya gaggauta kafa majalisar dokokin kasar.

Jamiyyar dake goyon bayan shugaba Pervez Musharraf ta sha kaye Zabubbukan majalisar dokokin da aka gudanar a kasar a watan Fabrairun da ya wuce.

Mr Musharraf ya bukaci gwamnati mai jiran gado da ta mance da batun siyasa kana ta yi jagoranci na gari.

Yarjeniyoyin game da gwamnatin hadaka za su shafi jamiyyar da marigayyiya Benezir Bhutto ke jagoranta  kafin ta rasu wato Pakistan Peoples Party da kuma jamiyyar Pakistan Muslim Party ta Nawaz Sherif. 

 

 
 
 

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m