Wani
jirgin sama mallakar kasar Iraki mai saukar ungulu ya rikito
kasa inda ya yi sanadiyar mutuwar wani sojin Amurka tare da wasu
mutane da ke cikin jirgin.
A wata
sanarwa da sojin kasar kasar suka bayar,sun ce jirgin kirar M-17
ya bace ne sakamakon rashin kyakkyawan yanayi a ranar
litinin,kana daga bisani aka tsinci jirgin a ranar Talata a
birnin Beiji mai nisan mil 90 daga kudancin Mosul.