Wani
dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin wani masallaci
dake yankin kudancin kasar Afghanistan da ta haddasa mutuwar mutane
akalla mutun 5 cikihar da mataimakin gwamnan jihar Helman
Babban
hafsan Rundunar yansanda dake lardin Muhammad Hussaini Andiwal
,ya ce dan kunar bakin wake ya tarwatsa bam din ne a lokacin da
ake salla a masallaci dake garin Lashkar Gah babban lardin na
Helman.
Mr
Muhammad Hussaini Andiwal ya ce Limamin masallacin na daya daga
cikin wadanda suka kwanta dama a harin.
Haji
Ikramullah wanda lamarin ya auku a agabansa saadda yake hanyar
zuwa masallacin ya ce ya ga gawarwawaki da kuma wadanda suka yi
raunuka ke ihu don neman agaji a masalacin.