Search Engine
 
 

Shafi.......................... Nijeriya ............... Afrika............... labaran duniya

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

Tel: 234- 01- 8799428

 

                LABARUN GIDA NIJERIYA

Shugaba Umaru Musa Yar Aduwa ya taya jiga-jigan shugabanin adawa guda biyu na kasar, wato Janar Muhahammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar

Alhaji Atiku Abubakar, bisa yadda suka yi azamar ci gaban tafarkin damakuradiya a kasar ta hanyar shigar da karar zaben da bai yi musu dadi ba.

Shugaba Yar Aduwa ya nuna farin cikinsa ga jama’a, kan yadda suka mika masa ragamar shugabanci. Shugaban ya nuna farin cikinsa ne sa’ilin da yake tarbar .wata babbar tawaga ta shugabannin jam’iyyarsu ta PDP, da gwamnonin jihohi da ministoci da kuma sauran masu taya shi murna a fadarsa ta Aso Rock dake Abuja.

Asusun bayar lamuni na duniya wato IMF ya yi kira ga kasashen Afrika da su yi koyi da Nijeriya wajen inganta harkokinsu na tattalin kudaden shiga.

Shugaban asusun  farfesa Dominik Skosan shi ne ya bayyana hakan a wani taron bita a Abuja babban birnin Nijeriya. Ya kara da cewa ka’idojin sarrafa kudaden da Nijeriya ke samu daga gurbataccen man fetur sun taimaka mata wajen gudanar da tattalin arzikin kasar. 

Gwamnan babban bankin Najeriya Farfesa Chukuma Soludo ya nuna damuwarsa bisa kokarin sauya fasalin tattalin arzikin kasar da aka kudura nan da shekara ta 2020, abin da ya ce rashin cikakken tsaro ka iya janyo masa cikas.

Soludo yayi wannan maganar ne a Abuja babban birnin Najeriya a yayin da yake gabatar ababan hawa na tsaro ga rundunar yan sandan Najeriya.


 
 
 

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m