Bincika
 

Shafi

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

Tel: 234- 01- 8799428

Shugaban Najerya Alhaji Umar Musa Yar adua, ya amince da murabus din da ministan kula da harkokin lafiya ta kasar farfesa Adenike Grange tayi gami da Ministan kasa a maaikatar Mr. Gabriel Adaku. 

Ministocin biyu dai zasu bar Majalisar zartarwar ta tarayya ne biyo bayan zargin cin hanci da hukumar kula da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta annati wato EFCC ta yi musu. 

Kwamitin kula da harkokin asusun hukumomi da maaikatun gwamnati a majalisar wakilai ta Najeriya, yayi yunkurin gano wurin da aka ajiye kudi kimanin Dalar Amurka Miliyan arba in, mallakar asusun bunkasa  fasahar manfetur. 

Wannan kudi dai shi ne abinda hukumar ta samu a matsayin rara wajen gasar samun rijiyoyin hako mai a shekarun 2004,2005 da kuma 2006, wanda kuma ba a sanya suba cikin  a cikin asusun hukumar, lamarin da ya sabawa dokar data kafa hukumar. 

Tashar Jiragen ruwa ta Houston dake a jihar Texas a kasar A kasr Amurka na son kulla  kawance da takwararta ta Najeriya da nufin bunkasa cinikayya tsakanin kasa da kasa.

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m