Bincika
 

Shafi

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

Tel: 234- 01- 8799428

An baiwa dukkan kamfanonin dake karkashin wani bincike da ake yi kan hada hadar kudade na shekarar ta 2005 a bangaren man fetir na Najeriya, makwanni biyu dasu bada cikakken hadin kansu wajan samar da bincike mai zaman kansa.

 A tattaunawar da tayi da kamfanonin da abin ya shafa a birnin Abuja hedikwatar Najeriya ,shugabar hukumar  tantance yadda kamfanonin kasar ke gudanar da ayyukansu(NEITI) Farfesa Assisio Asoubio, ta ce an dauki wannan mataki ne da nufin tabbatar da cewa  an gudanar da binciken  yadda ya kamata.

 

Jamian hukumar bunkasa yankin Naija-Dalta sun kara jaddada bukatar dake akwai ta ganin an tabbatar da bin ka’idojin da suka dace wajen bayar da kwangilar sake gina yankin.

Kwamishinan hukumar mai kula da jihar Ondo kudu maso yammacin  Najeriya Ibukun Omotohinshe,shine ya bayyana haka a babban birnin jihar dake Akure.Yace daukar wannan mataki ya biyo bayan munanan matakan da aka shimfida a baya  game da bayar da kwangila kana daga bisani a yi watsi da ita.  

 

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m