Shugaban
Nijeriya Alhaji Umaru Musa Yar’adua ya bukaci al’umomin kasar da
su yi anfani da ranakun bukukuwan idil maulud da kuma Ista a
matsayin wata damar yin tunani mai zurfi game da koyarwa da kuma
akidun addinin Islama da kuma na kirista.
Bayanin
hakan na kunshe a sakonsa ga al’umar Nijeriya na barka da idil
maulud da kuma ista na wannan shekarar.
Shugaban
yace galibin yan’ kasar na bin daya daga cikin addinan biyu mafi
girma a kasar.
Mataimakin
Shugaban Nijeriya ,Dr Goodluck Jonathan ya bukaci al’umomin
kasar da su dukufa domin bautawa Allah da kuma yi wa kasa
hidima.
A sakonsa
ga mabiya addinin kirista a Nijeriya,Mataimakin shugaban yace su
kekashe kasa don ganin ana gudanar da duk wani abu akan kai’da.
Gwamnatin
Jihar Bauchi Arewa maso gabashin Nijeriya ta kebe fiye da Naira
Miliyan dubu biyu da rabi domin samar da ruwa mai tsabta ga
al’umar jihar cikin watanni 10 da suka gabata.
Kwamishinan kula da albarkatun ruwa na jihar,Alhaji Tanko Dutse
ne ya bayyana haka a garin Bauchi babban birnin jihar.