Bincika
 

Shafi

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

Tel: 234- 01- 8799428

 

Mai Magana da yawun maaikatar harkokin wajen nijeriya ya bayyana cewar jagorancin kasar a kwamiti na musamman kan wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya baya fuskantar barazana.

A yayin da yake maida martini a dangane da batun sahihancin jagorancin kasar a kwamitin ayyukan zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a Abuja fadar gwamnatin nijeriya, Mr. Olukanni yace dan tsaikon da aka samu na tura babban jakadan kasar zuwa majalisar dinkin duniya bai kawo wani babban gibi ba gami da shafar kasar wacce ta shafe shekaru goma tana shugabancin kwamitin tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniyar.

Kazalika Mr. Olukanni yace wannan karramawar da aka yiwa kasar ya biyo bayane a dangane da irin rawar da kasar take takawa tun  shekarar 1960 a matsayin  wata kasa dake da dakarun wanzar da zaman lafiya masu yawa na majalisar dinkin duniya, haka kuma Mr. Olukanni ya kara da cewar a yanzu haka nijeriya tana da jakadu a wasu manyan kasashe kamar su Jamus, Beljium, Habasha. Israila, Indiya, Swiziland gami da ofishin majalisar dinkin duniya dake a Geneva. 

Aranar laraban nan ne musulmi  a duk fadin duniya suka gudanar da bikin  tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta annabi  Muhammmad  tsira da amincin allah su tabbata a gareshi.

 Wannan ranar dai musulmai  na amfani da ita ne domin gudanar da karatun Alqurani mai girma gami da yin nazarin kyawawan dabiun fiyayyen halitta annanabi mohammad tare da karanta litattafan addini a duk daukacin daren ranar goma sha biyu ga watan Rabiul awwal, wanda ya kasance wata na uku dake a cikin kalandar addinin musulunci.   

An kalubalanci maaikatan  jarida da su kawar da  munanan manufofin da ake alakantawa ga addinin Islama.

Shugaban kungiyar kafafen yada labaru ta Najeriya (BON) Alhaji Abubakar Jijiwa shi ne yayi wannan kiran a Abuja babbab birnin tarayyah a yayin taron tunawa da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.W.A.) da kungiyar musulmai yan jaridu nijeriya ta shirya a abujan.

A cikin wadanda suka sami dammar halartar taron ciki hadda babban jakadan kasar parisa a nijeriya sai mr,isah cosuro kesasaga gami da wasu futattun yan jaridu dake a nijeriya.

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m