Ofishin
kula da samar da ayyukan bunkasa walwalar jama a na
Najeriya,wanda aka fi sani da ofishin bin matakan da suka
dace,ya bayyan cewa ya rigaya ya amince da mika tsabar kudi fiye
da dalar Amurka miliyan dubu biyar da miliyan biyar dan biyan
yan kwangilar da suka gudanar da ayyukansu na makamashin wutar
lantarki a kasar a tsakanin shekara ta 2003 zuwa ta 2007.
Shugaban
Majalisar Dattawan Najeriya David Mark yayi Allahwadai da yadda
harkar samar da wutar lantarki take tabarbarewa a kasar
Can a
Abuja fadar gwamnatin Najeriya ne shugaban majalisar ya yi
wannan furuci ,a yayin wani taron bita kan harkar yin doka da
bukatar samar da dokar makamashin Nukiliya a kasar.