Bincika
 

Shafi

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

Tel: 234- 01- 8799428

Ministan kula da aikin gona da albarkatun ruwa a Nijeriya Dakta Abba Sayyadi Ruma ,ranar talatar nan 18 ga watan Maris shekara ta 2008 ya yi bayani ga taron manema labaru game da ranar ruwa ta duniya da kuma kaddamar da ranar tsabtace muhalli ta kasa da kasa.

Wakilin Asusun kula da harkokin yara na Majalisar dinkin duniya wato UNICEF Mr Ayalew  Abai da wasu shugabanin hukumomin Majalisar dinkin duniya dake Nijeriya da Kungiyoyi masu zaman kansu da kuma masu ruwa da tsaki ne suka halarci taron. 

Kotun sauraron kararrakin zabe a Nijeriya ta amince da zaben gwamnan jihar Oyo kudu maso yammacin Nijeriya Cif Adebayo Alao-Akala.

Duk da cewa Alkalai uku na kotun sun amince da zaben,daya daga cikinsu ya bukaci a soke zaben sabili da an hana wasu yancin kada kuria.

Dan takarar neman mukamin gwamna karkashin jamiyyar A.N.P.P. M r Abiola Ajumobi ne ya hade da wasu jamiyyu biyar na yan adawa domin kalubalantar zaben Cif Adebayo Alao-Akala wanda aka zaba watan Afrilun shekarar 2007.

Masu karar sun yi ikirarin cewa kwamitin binciken da tsohon gwamnan jihar Oyo Alhaji Rashid Ladoja ya kafa ya samu gwamna Aalao-Akala da laifin aikata ba daidai ba..

Yan adawar suna masu tambaya game da yadda gwamnan  ya bar aikin dansanda wanda aka yi masa ritayar dole domin ladabtarwa sakamakon laifin da ya aikata.. 

Shugaban kwamitin kula da harkokin muhalli na majalisar dokokin jihar Lagos kudu maso yammacin Nijeriya Mr Adesina Ogunkoya, ya bayyana cewa gwamnati ta ware Naira miliyan 500 domin inganta magudanun ruwa na jihar.

Mr Adesina Ogunkoya  ya fada a birnin Lagos cewa zaa yi amfani da kudin domin samar da magudanun ruwa da kuma yashe mashigan ruwa  a tsawon kilomita 52.

Shugaban kwamitin kula da muhalli ya ce hukumomi a jihar sun shirya

Tsab domin yin amfani da kudin wajen ginawa da kuma yashe magudanun da kuma wasu mashigan ruwa,da nufin maganta matsalar ambaliyar ruwa.a Birnin Lagos da kewaye.

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m