Bincika
 

Shafi

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

Tel: 234- 01- 8799428

Kwamitin kula da harkokin makamshi da karafa  na majalisar wakilan Nijeriya ya ci gaba da sauraron baasi game da makudan kudin da tsohuwar gwamnatin kasar ta kashe kan ayyukan lantarki ba tare da an tabuka wani abin kirki ba.

Mambobin kwamitin a majalisar wakilai sun bayyana takaicinsu game da bude tashar lantarki ta wucin gadi a Abuja babban birnin Nijeriya, a shekarar 1999.

Kazalika yan majalisar sun nuna takaicinsu game da bayanin da wani jamiin kamfanin lantarki na kasar Alhaji Shuaibu  Maigida ya yi game da tashar wucin gadin a Abuja.

Shugaban kwamitin Mr Ndudi Godwin Elumelu ya bayyana takaicin cewa gwamnatin kasar ta bada fiye da dola miliyan dubu biyu da rabi ba tare da an yi wani aiki na a zo a gani ba. 

Majalisar dattawan Nijeriya ta umarci kwamitinta mai kula da harkokin babban birnin Nijeriya Abuja da ya yi binciken sayar da kaddarorin gwamnati da raba filaye da soke takardun mallakar filaye da aka yi a yankin Abuja daga shekarar 1999 zuwa yanzu.

Kazalika kwamitin zai sake duba harkokin da suka shafi babban asibitin Garki da filin shakatawa na Abuja da kasuwar Wuse da kamfanin NICON da Otel din Sheraton.

Sauran kuma su ne hukumar kula da sufuri ta birnin Abuja da hukumar kula da raya yankin Abuja.

Shugaban kwamitin kula da harkokin yankin Abuja na majalisar dattawa sinata Abubakar Sodangi wanda ya gabatar da kudurin a majalisar ya bayyana cewa bai ji dadin yadda hukumomin baya na babban birnin Nijeriya Abuja suka gudanar da harkokin birnin ba.    

Kwararru a fanin lantarki dake Nijeriya sun bukaci hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar da kamfanoni masu zaman kansu domin samarwa,sarrafawa da kuma raba makamashi a kasar.

Wannan mataki na da nasaba da matsalolin lantarki da Nijeriya ke fuskanta domin amfani da shi a masanaantu da kuma harkokin yau da kullum.

Masanan sun lura cewa hadin gwiwar zai inganta fanin lantarki da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.

Wani mamba a kwamitin kula da harkokin lantarki na majalisar wakilai Mr Buraimoh Ajibola,ya ce yan Nijeriya su tallafawa yunkuri na gwamnati ta hanyar kulawa da kaya da kuma naurorin lantarki dake fadin kasar.

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m