Hausa Archive

 
Search Engine
 
 

Shafi.......................... Nijeriya ............... Afrika............... labaran duniya

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

 

Ranar Litinin 10 ga watan Maris wakilai na Tarayyar Turai E.U. da abokan hadin gwiwa guda 2 na Majalisar dinkin duniya za su yi taro da kuma tatance ci gaba da Nijeriya ta samu game da samar da ruwa mai tsabta da kuma kula da muhalli a kasar.

Bayanin haka na kunshe a wata takardar sanarwa da asusun kula da harkokin yara na majalisrdinkin duniya wato UNICEF ya gabatar a babban birnin Nijeriya.

Takardar sanarwar na dauke da sa hannun masanin harkokin sadarwa,kafafan yada labarai da hulda da kasashen ketare na UMICEF dake Nijeriya, Mr Geoffrey Njoku. 

Gwamnatin Nijeriya ta aike sakon taaziyya ga al-ummar jihar Katsina dake arewacin Nijeriya sabili da rasuwar Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Muhammad Kabir Usman.

A maraicen asabar nan ne aka yi jana izar marigayin a Katsina wanda ya rasu a safiyar ta asabar a babban asibitin kasa dake Abuja hedkwatar Nijeriya.

Mataimakin shugaban Nijeriya Dr Goodluck Jonathan wanda sakataren gwamnatin kasar      Alhaji Babagana Kingibe da wasu kusoshin gwamnatin kasar suka rufa masa baya ne ya jagoranci tawagar zuwa fadar Sarkin domin yin gaisuwar taaziyya.

Gwamnan jihar Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema da kuma wasu manyan baki ne suka tarbi ayarin na gwamnatin Nijeriya.

 

 
 
 

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m