Hausa Archive

 
Search Engine
 
 

Shafi.......................... Nijeriya ............... Afrika............... labaran duniya

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

 

Darakta janaral kuma mataimakin sakataren hada hadar ciniki da kasuwanci na kasar Amurka Isra’il Hernendez zai jagoranci wata tawaga zuwa wasu kasashen nahiyar afrika,ciki har da Nijeriya da nufin kulla yarjejeniyar huldar kasuwanci a kasashen. 

Har ila yau tawagar ta hada da jami’an kanfanoni 13 na kasar Amurka wadanda zasu zu neman abokan huldar cinikayya a Nijeriya. 

Mr Hernaendaz ya bayyana fatansa na jawo wasu manya kuma ingantattu kanfanonin a kokarinsa na kulla huldar cinikayya ga kasar Ghana,Nijeriya,da kuma Afrika ta kudu. 

Gwamnatin Nijeriya za ta daukaka darajar wasu filayen tashi da saukar jiragen sama  na kasa da kasa da nufin gudanar da hada hadar su cikin sauki. 

Ministan kasa a ma’aikatar jiragen sama Felix Hassan Hyet shi ne ya bayyana haka ga manema labaru a bayan wata tattaunawa da shugaban Nijeriya Alhaji Umaru Musa Yar’adua ya yi da masu ruwa da tsaki a harkokin hada hadar jiragen sama da ya gudana a Abuja hedikwatar kasar. 

Filayan tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa da za a daukaka darajar su sun hada da na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja babbam birnin Kasar,sai na Mallam Aminu kano a jihar Kano arewa maso yammacin Nijeriya,kana da na jihar Legas kudu maso yammacin kasar,a karshe da na Fatakwal da ke kudancin kasar.

 
 
 

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m