Search Engine
 
 

Shafi.......................... Nijeriya ............... Afrika............... labaran duniya

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

 

Gwmnatin Najeriya ta yunkura domin sake yin nazari game da dokokin yawon bude ido
da kuma al adu na kasar.

Ministan yawon bude ido ,aladun gargajiya da wayar da kan jamaa a Najeriya,Yerima Adetokunbo Kayode shine ya bayyana hakan a Abuja babban birnin Najeriya.

Ministan ya ambata wadanan kalaman ne yayin da yake yiwa manema labari bayani game da alkibilar da maakatarsa ta sanya gaba a shekara ta 2008.

Yerima Kayode y ace hukumomi a Najeriya za su rinka sabunta kaidodi dakuma dokokin da suka shafi fanonin yawon bude ido,aladun gargajiya domin su dace wannan zamani.

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa a Najeriya wato NAFDAC, ta dukufa domin ganin ana buga gargadi ballo-ballo a fakitin sigari ga masu zukar taba.

Darakta janar ta hukumar, Farfesa Dora Akunyili,,it ace ta bayyana hakan a hedkwatar kasar Abuja yayin wan taro na kasa game da matasa.

Farfesa Dora Akunyili ta bayyana takaici game da wasu da suka rungumi akidar shan taba a tsakanin jamaa..

Ta ce hukumar NAFDAC za ta aike sakonni ga kamfanonin sigari don su buga sakonnin gargadi dalla-dalla a fakitin sigari.


 
 
 

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m