Hukumar
kula da harkokin makamashin Niukiliya a Nijeriya ta fara bayar
da horo ga Jamianta domin tabbatar da kariya wajen yin amfani da
cibiyoyi da kayayyakin makamashi a Kasar.
Wannan
horon dai na gudana ne tare da hadin gwiwar Hukumar kula da
makamashin Niukiliya ta Duniya,mai mazauni a Birnin Vienna na
kasar Austria.
A lokacin
bukin bude taron bayar da horon,Shugaban hukumar a
Nijeriya,Farfesa Shamsuddeen Elagba,yayi nuni da cewar horon zai
bunkasa yin amfani da makamashin Niukiliya domin samar da wutar
lantarki.
A nashi
jawabin,wakilin hukumar kula da makamashin Niukiliya ta kasa da
kasa,Dakta Rustin Passi,wanda kuma daya ne daga cikin masu
bayar da horon ,ya bayyana cewar hukumar kula da makamashin
Niukilya ta kasa da kasa zata taka rawar kayyade bada lasisi da
sanya – ido da kuma kayyade daukacin aikin hukumar.
Ofishin
Jakadancin Nijweriya dake kasasr Birtaniya ya karrama wasu yan
Nijeriya guda biyu saboda ficen da suka yi a kasar.
Wadanda
Ofishin ya karrama dai,sune Ibrahim Baba Shehu da Chinwe
Chiduben dake karan jamia a kasar ta Birtaniya sakamakon rawar
ganin da suka taka a jamioin da suke karatu.