Search Engine
 
 

Shafi.......................... Nijeriya ............... Afrika............... labaran duniya

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

Tel: 234- 01- 8799428

 

                  LABARUN DUNIYA

Shugaban adawar kasar Kenya Raila Odinga yayi kira ga magoya bayansa da su janye zanga-zangar da aka shirya yi don hura wa gwamnati wuta akan shirin raba madafan iko domin kawo karshen rikice-rikicen zaben siyasar kasar.

Mr Odinga ya shaidawa manema labarai cewar jam’iyarsu ta ODM ta gamsu da ganawar da suka yi da tsohon  maga-takardar majalisar dinki duniya Kofi Annan. A saboda haka ne suka janye zanga-zangar da suka yi niyyar yi har zuwa wani lokaci. 

A Khartun kuma babban birnin Sudan dubun dubatar mutane ne suka yi zanga-zangar nuna bacin rai game cin zarafin da aka yi wa addinin Musulunci ta hanyar buga wani hoto da suke cewa ma’aiki ne.

An sake buga hoton cin zarafin ne bayan shekaru biyu da suka wuce wato a shekara ta 2006. Wanda hakan ya haddasa zanga-zanga a duniya baki daya.

 

              

 
 
 

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m