Daruruwan
mata ‘yan asalin kasar Laberiya dake zaune a Ghana sunyi watsi
da zaman makwanni biyar na nuna kin amincewar su da shirin
komawa gida.
Matan sun
kawo karshen wannan kin amincewa a sansanin Buduburan dake
tsakiyar kasar bayan da jakadan Laberiya ya kai masu ziyara.
An nuna
kin amincewar ne da nufin nuna kin amincewa da shirin nuna
rashin goyon baya ga shirin majalisar dinkin duniya na bada
dalar Amirka dari daya ga kowannansu domin su koma gida
Laberiya.
A karshen
makon daya gabata dai an maida mazaje goma sha shida zuwa birnin
na Monrobiya
Kazalika
jakadan kasar tasu dai yayi masu alkawarin mika dukkanin
bukatunsu ga mahukuntan kasar Ghana dana majalisar dinkin
duniya.