Shugaban Kuwaiti ya rushe
majalisar dokokin kasar a daidai lokacin da kasar ke fama da
rikice rikicen siyasa lamarin da yayi sanadiyyar saukar ‘yan
majalisar zartarwar kasar baki daya.
A ranar 17 ga watan Mayu ne ake
saran zaa sake sabon zabe a kasar
wacce keda albarkatun mai.
Sheikh Sabbah ya ambata hakan
bayan wata gajeriyar ziyara zuwa kasar Morocco da nufin kawo
karshen wannan takaddama.