Hausa Archive

 
Search Engine
 
 

Shafi.......................... Nijeriya ............... Afrika............... labaran duniya

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

 

Shugaban Amirka George W.Bush ya bayyana shirin rarraba Gidan sauro da nufin tseratar da kananan yara daga wannan cuta ta zazzabin cizon sauro wacce ke kisa.

A rana ta uku cikin rangadi da yake a kasashen Afrika guda biyar,shugaban yaje arewacin Tanzaniya da nufin maida hankali wajan kawo karshen wannan cuta da tayi sanadiyar rasuwar akalla jarirai miliyan daya gami da kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin na Afrika dake da sahara.

Cikin kira da akeyi na kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro a Afrika,shugaba Bush ya bayyana sabon tsarin bisa hadin gwiwar bankin duniya na bada Gidan sauro sama da miliyan biyar a kasar.

Harilayau ya kuma bayyana cewa  shirin na dakile wannan cuta wanda za a fara watanni shida nan gaba zai bada isassun gidajen sauro da zasu bada kariya ga yara kanana ‘yan kasa da shekara daya zuwa biyar.A watan yulin shekarar 2005 ne  shugaban ya fitar da shirin na dakile cutar a kasashen Afrika wanda zai lashe dalar Amirka sama da miliyan dubu guda da nufinrage rashe rashen rayuka zuwa kashi goma sha biyar daga cikin dari ta sanadiyar wannan cuta.

 

 
 
 

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m