Bincika
 

Shafi

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

Tel: 234- 01- 8799428

Kasar Birtaniya ta kare kanta dangane da mataki da ta dauka na maida ‘yan kasar  Zimbabwe masu neman mafaka  zuwa ga kasarsu ta haihuwa.

Kimanin ‘yan kasar dari biyar ne suka karbi takardunsu na neman su gaggauta komawa gida  ko kuma su fuskanci tilastawa daga bangaren hukumomin Burtaniya.

Cikin wadannan mutane wani ya bayyana cewa abin mamaki ne ga Birtaniya ta yi watsi da cin zarafin alummar kasar da akayi a baya  kana ta yi kokarin tilastawa mutane komawa gida.

Sarah Harland ta gano cewa kiran babban zaben kasar wanda aka shirya yinsa anan gaba,abune wanda aciki  ake saran  aikata adalci.

Har ila yau Uwargida Sarah mamba cikin wata kungiya dake kasar wacce ke taimakawa  wadanda suka rasa mafakar  ta bayyana cewa akwai bukatar canji ainda ta kara da cewa maida wadannan mutane kasar a halin yanzu abune wanda bai dace ba.

Kungiyar fafutikar hakkin bil Adama dake birnin New York na kasar Amurka ta bayyana cewa rikicin kabilanci daya biyo bayan Zaben shugaban kasar Kenya a watan Disambar bara abune da aka kirkiro shi .

Kungiyar ta ce kai farmaki kan  alummar kikuyu ta shugaba Mwai kibaki abu ne da sarakuna suka kulla makarkashiya a matsayin maida martini kan abokan adawaarsu .

Wannan kungiya ta bukaci da a gaggauta gabatar da wadannan  shugabanni  a gaban kuliya manta sabo bisa laifin sanya hannaye wajan tayar da tarzoma wacce tayi sanadiyyar kisan sama da mutane dubu daya da kuma sanya wasu jamaa sama da dubu dari shida  su kauracewa gidajensu.

Kazalika rahotanni  sun dora alhakin ga jamian ‘yansanda  wadanda suka yi amfani da karfi fiye da kima kan ‘yandawa saadda suke zanga zanga .

Tuni dai dan adawa Raila Odinga ya sa hannu kan yarjejeniyar raba madafun iko  da shugaba Mwai Kibaki wanda kuma kungiyar tayi murna da yin hakan.

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m