Bincika
 

Shafi

Barka da zuwa Muryar Nijeriya ............................ Sashen Hausa

Turo E-Mail

Tel: 234- 01- 8799428

Gwamnatin Cadi ta ce dakarun yan tawaye dauke da miyagun makamai sun shige mata kasa ta gabashi daga Sudan.

Wata sanarwa ta Gidan rediyon kasar ta ce sojojin hayar sun tsallaka iyakarta ne a yankin Moundeina,arewa da iyakar garin Ade.

Idan ba a manta ba a watan jiya yan tawaye sun yi wani kokarin da ya ci tura na kifar da gwamnatin Shugaba Idris Derby.

Yanzu haka Shugaba Idris Derby da Shugaba Omar al-Bashir na Sudan sun sa hannu akan wata yarjejeniyar hana goyon bayan yan tawayen wajen kai hari cikin kasashen juna.

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Mr Ban Ki-Moon shi ne ya shugabanci sa hannu kan yarjejrniyar a Dakar babban birnin kasar Sinigal.

 

Gwamnatin Sudan ta yi fatali da sukar da Amurka ta yi cewa Sudan na take hakin bil Adam.

Sudan ta ce gwamnatin shugaba George Bush ce tafi kowace kasa game da take hakkokin dan Adam kuma mai bakin ciki da duk wasu ayyukan ci gaba da hukumomi a birnin Khartoum suka samu.

Wata majiyar Amurka ta bayyana cewa ana ci gaba da kashewa da kuma azabtar da mutanen da ba su ji ba, ba su gain ba da kuma yiwa mata fyade.

 

Home | Contact | VON | Contact Us | archive
Webmaster@voiceofnigeria.org :Change Password :VON Staff Sign Up
Copyright© 2007. All Rights Reserved Voice Of Nigeria. Developed by: VON ON-LINE

7255KHz 41m; 9690KHz 31m; 11770KHz 25m; 15120KHz  19m