Mahaukaciyar guguwar nan wato JOKWE ta lalata kusan gidaje 500
da kuma kashe mutun guda a yankin arewacin kasar Muzambik, a
ranar lahadin nan.
Shugaban sashen kula da yanayi na kasar,Musa Mustafa, ya ce
guguwar ta yi mummunar ta adi a tsibirin Madagasca.Musa Mustafa
ya ce mai yiwuwa guguwar Jokwe ta kara yin wata barna a litinin
nan.
Hukumar kula da shaanin dokoki a kasar Afrika ta kudu ta gabatar
da sabon tsarin da zai lalubo dokokin da suke da alaka da nuna
wariya a kasar.
Tsarin zai yi gyare-gyare akan dokoki 2,800 wadanda aka kafa a
kasar tun daga shekarar 1910.
Wata Alkali a kotun tsarin mulkin kasar Afrika ta Kudu,Yvone
Mokgoro ta ce babban dalilin gabatar da wannan sabon tsari shine
maida samar da dokokin da za su dace da zamani.
Kazalika wasu kwararrun ahrkokin dokoki za su bada tasu
gudumowar domin gabatar da tsarin mulkin da ya soke dukkan sassa
masu alaka da nuna wariyar launin fata a kasar.