Babban
magatakardar majalisar dinkin duniya Mr Ban Ki-Moon ya yi kira
ga shugabanni a kasashen Sudan da Cadi da su inganta matakan tsaro
,daiadai lokacin da gwamnatin jumhuriyar Cadi ta ce yan tawaye
sun kara kusantar birnin Njamena hedkwatar kasar.
Mr
Ban Ki-Moon ya yi wannan tsokacin ne a kasar Habasha, yana mai
cewar ,tsaurara tsaro na da mahimmanci sabili da yan tawaye sun
kutsa kai a yankin gabashin cadi.
Ya
bukaci kasashen Cadi da Sudan da su sanya ido sosai game da jamian
tsaro dake iyakokinsu.
Kasashen
2 na zargin juna da tallafawa yan tawayaen.
Kungiyar Tarayyar kasashen Afrika wato A.U. ta zabi shugaban kasar
Tanzania Mr Jakaya Kikwate a mukamin sabon shugabanta.
Yayin
taro karo na 10 wanda shugabannin gwamnatoci da kasashe suka yi
a Adia-Ababa babban birnin kasar Habasha ne Kungiyar ta A.U. ta
zabi Mr Kikwate.
A
jawabinsa ga Tsohon shugaban A.U. Mr John Kuffour na kasar Ghana
ya bukaci a maida hankali sosai akan sake maida zaman lafiya da
lumana a kasashen Sudan da Somaliya da kuma sauran sassan nahiyar
ta Afrika.