Bangarorin
siyasar dake takun saka a kasar Kenya,sun sha alwashin hanzarta
yin tattaunawa da nufin warware takaddamar da suka dade suna yi
akan arziki da filaye ,sanadiyyar rigingimun da suka biyo bayan
zabukan kasar wanda kuma ya zubar da martabar ta a matsayin
daya daga cikin kasashen afrikar dake da daidaiton shaanin
siyasa.
Alummar
kasar Kenya dai,bayan tayi fama da matsalolin sace-sace,da
kone-kone da kuma kasha-kashen kabilanci,sakamakon takaddamar
data biyo bayan Zaben ranar ashirin da bakwai dga wata Disambar
bara,a yanzu ta yi marhabin lale da gwamnatin hadin kan
kasa,wadda aka cimma yarjejeniyar kafa- ta a makon da ya
gabata,domin kawo karshen tashin hankalin da ya fatattaki masu
yawon bude-ido a kasar ,kana da janyo koma-baya ga tattalin
arzikin kasar.
Yarjejeniyar,wadda tsohon Sakataren Majalisar dinkin duniya Mr
Kofi Annan,wanda kuma shine babban mai shiga tsakani ya
jagoranci kulla ta,zata dubi batun filaye da samar da
sauye-sauye ga shaanin Zaben kasar.
Mr
Annan,wanda ya mika aikin shiga tsakanin ga tsohon ministan kula
da harkokin ketare a Nijeriya Farfesa Oluyemi Adeniji,ya
bayyana cewar kamata yayi a warware dukkan batutuwan da aka dade
ana jayayya akan su cikin waadin shekara guda,amma yan siyasar
da ake tattaunawa dasu sun bayyana cewarsuna fatan hanzarta
aikin su.